(ABNA24.com) Kasar Faransa ta sanar da hallaka jagoran kungiyar Al’Qaida a yankin arewacin Afrika da sahel a wani samame da sojinta suka kaddamar a arewacin kasar Mali.
Da take sanar da hakan a shafinta na twitter, ministar tsaron Faransa, Florence Parly, ta ce an hallaka Abdelmalek Droukdal, jagoran kungiyar ta AQMI, da kuma wasu na hannun damansa a ranar Laraba data gabata.
An hallaka Abdelmalek Droukdal, ne yayin wani samame na hadin guiwar sojojin Faransar da abokan huldarsu na yankin a cewar Florence Parly.
Ministar tsaron ta Faransa, ta bayyana wannan a matsayin wata babbar nasara a fafatukar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
An bayyana Abdelmalek Droukdal, a matsayin babban kwamandan rassan kungiyar Al’qaida a arewacin Afrika da yankin Sahel ciki har da kungiyar nan ta JNIM, data yi kaurin suna wajen kai hare hare a yankin sahel.
/129
6 Yuni 2020 - 05:43
Lambar labari: 1043643
Kasar Faransa ta sanar da hallaka jagoran kungiyar Al’Qaida a yankin arewacin Afrika da sahel a wani samame da sojinta suka kaddamar a arewacin kasar Mali.